Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; Harin da HKI ya kawo wa Iran take diflomasiyya ne, da kuma dokokin kasa da kasa, don haka tattaunawa da Amurka bai taba zama an gina shi akan gaskata ta, ko yarda da ita ba.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ma’aikatar harkokin wajen na Jamhuriyar musulunci ta Iran ya ce; kallafawa Iran yaki, yana daidai da hargitsa zaman lafiya a cikin wannan yankin ne na yammacin Asiya.
Dr. Isma’ila Baka’i ya kara da cewa, Abinda ya faru, bai tsaya a kasantuwarsa take diflomasiyya kadai ba, ya kuma sake rusa duk wata gaskatawa da yarda da Amurka, idan har akwai ta.
Dr. Baka’i ya kuma ce; Ina sake jaddada cewa, dama can ba mu zauna da Amurka akan teburin tattaunawa ba saboda mun yarda da ita,domin ta shahara da cewa ita mai karya alkawali ce, akan Shirin Iran na makamashin Nukiliya.