Dan majalisar dokokin kasar labanon mai wakiltar kungiyar gwagwaramaya ta hizbullah hassan fadlallah ya caccaki gwamnatin labanon na kasa tabuka komai game da ta’asar da gwamnatin isra’ila ke yi na kai hare hare a kudancin kasar, kana ya jaddada cewa bai kamata gwamnati tayi watsi da hakkin alummar kasar na kare kansu ba, tun da ba za ta iya karesu daga zalunci isra’ila ba
Har ila yau Hassan fadlullah yace kafin tattaunawa game da batun ikon sarrafa makamai ko kuma zabi tsakanin yaki da zaman lafiya ya dole ne gwamnati ta tabbatar da tsaro a cibiyoyin gwamnati a kudancin labanon, yace kungiyar hizbullah a shirye take a bude tattaunawa game da batun tsaron kasa idan sojojin isara’ila suna janye daga dukkan yakunan da suka mamaye a kudancin kasar
har ila yau dan majalisar ya soki yarjejeniyar da aka kulla a watan yuni tsakanin labanon da HKI ,inda aka gudanar da ita ba tare da tuntubar kwararru ba sai dai kawai aka ji labarin a sanya hannu, yace kasar iran ta samar da sabon tsarin dakile makiya a yankin yammacin asiya don haka ya kamata gwamnatin labanon ta yi amfani da wannan yanayin.