Jakadan Jumhuriyar Musulunci ta Iran (JMI) na din din din a majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa Tehran ba za ta taba manta da yan makarantar Ashsjaratul Tayyibah na garin Minab a kudancin kasar Iran ba, inda Amurka ta jefa boma bomai kan makarantar a ranar 28 ga watan Fabrayru na wannan shekara ta 2026 da muke ciki. Ta Kashe mutane 168 yan makaranta da malamansu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Jakadan kasar Iran a majalisar yana fadar haka, a jiya jumma’a a bikin ranar yara ta duniya, ya kuma kara da cewa, ko wani yaro a duniya yana da hakkoki na asasi wadanda suka hada da kariya, karatu, sannan uwa uba rayuwa, da kuma kyautata rayuwansa na gaba da kuma shiryawa gurinsa a rayuwa.
Ali Bahraini ya kara da cewa, ya zuwa yanzu yan makarantar Minab kimani 300 da suka tsallaka rijiya da baya a hare haren na Amurka suna rayuwa a rikice, don suna bukatar lokaci kafin su dawo cikin hayyacinsu..
Sojojin Amurka a ranar farko na yakin da suka dorawa JMI, wato 28 ga watan Fabrayru na wannan shekara sun jefa ‘Uwar Boma Bomai a kan makar