Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya ce asibitoci ba sa aiki a arewacin yankin da aka yi wa kawanya.
Sojojin Isra’ila sun ba da umarnin ficewa tare da kara kai hare-hare a ‘yan kwanakin nan yayin da suka kaddamar da wani sabon farmaki ta kasa a arewacin Gaza, tare da raba kimanin mutane 100,000 da muhallansu, a cewar MDD.
A sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia an yi kazamin fada tsakanin sojojin Isra’ila da kungiyoyin Falasdinu.
Fararen hula da suka rasa matsugunansu sun ce halin da ake ciki yayin matukar muni”, yayin da sojojin Isra’ila suka yi ta luguden wuta kan matsuguna na hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta UNRWA tare da tilasta wa dimbin jama’a yin gudun hijira.
Alkalumman da ma’aikatar lafiya ta Gaza ta fitar a jiya Litini sun nuna cewa adadin falasdinawan da suka rsa rayukansu a hare-haren Isra’ila ya zarce 35,000.