Larijani: Iran Ba Zata Taba Mika Wuya Ba

Babban sakataren Majalisar Kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba mika wuya ba Babban sakataren majalisar koli

Babban sakataren Majalisar Kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba mika wuya ba

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya yi jawabi ga al’ummar yahudawan sahayoniyya kan abubuwan da suka faru a lokacin tsagaita bude wuta, da kuma kalubalen da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke fuskanta a cikin wadannan kwanaki gami da yadda za a tafiyar da su. Ya jaddada cewa; Iraniyawa ba za su taba mika wuya ba.

A hiransa da Shafin KHAMENEI.IR, Ali Larijani ya yi tsokaci kan abubuwan da suka faru a lokacin tsagaita bude wuta da yahudawan sahayoniyya, batutuwa da kalubalen da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke fuskanta a wadannan kwanaki da kuma yadda za a tafiyar da su. Wadannan batutuwan sun hada da tattaunawar makamashin nukiliyar Iran da ayyukan kwamitin koli na tsaron kasa, da fagen tsayin daka, da hanyar da za ta haifar da rudani, da yarjejeniyar Azarbaijan da Armeniya, da magance gibin tsaro, da karfafa karfin kai hare-hare na soja, da gudanar da harkokin siyasa da kafofin watsa labaru, da babban fifikon kasar wajen warware matsalolin kasar.

A cikin hirar, Ali Larijani ya bayyana cewa, babban aikin kwamitin koli na tsaron kasar Iran, shi ne tafiyar da kalubale ta yadda zai samar da yanayin zaman lafiya ga ci gaban kasa, da bai wa al’ummar kasar damar more rayuwar da za a iya hasashensu, kamar yadda a ko da yaushe akwai kalubale.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted