Babban Kwamandan Sojojin Iran Ya Sanar Da Tsarin Sabunta Matakan Mayar Da Martani Kan Makiya

Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Sun sabunta hanyoyin da sojojin Iran zasu mayar da martani kan duk wani harin wuce gona da

Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Sun sabunta hanyoyin da sojojin Iran zasu mayar da martani kan duk wani harin wuce gona da iri kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bada umarni

Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdur-Rahim Mousawi ya bayyana cewa: Tun tsawon kwanaki da suka gabata jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewa: Idan Amurka ta farma tsaron al’ummar Iran, to lallai Iran za ta kai farmaki kan tsaronta ba tare da wata shakka ba, wannan ya kasance umarni ne bayyananne ga dakarun Iran, kuma kwamandojin sun sabunta shirinsu na aiwatar da wannan umarni, kuma a halin yanzu Iran a shirye take tsaf don gudanar da umarni a aikace.

Manjo Janar Mousawi ya kara da cewa: Sun sha wahalhalu da dama, kuma makiyansu sun yi kokari da dukkan karfinsu a cikin shekaru 46 da suka gabata don dakile juyin juya halin Musulunci da ruguza shi da karkatar da alkiblarsa, amma wannan al’umma karkashin jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci da jinin shahidan ta, ta ci nasara kan dukkanin wadannan makirce-makircen da alfahari da nasara.

Mousawi ya jaddada cewa: Su al’umma ce da ke cewa sun nisanta daga karbar wulakanci, kuma sun yi alkawari ga Allah Madaukakin Sarki, da jagoransu da kasarsu mai albarka da kuma al’ummarsu masu zurfin hankali da basira gami da hakuri da jinin shahidan Iran 200,000, wadanda suka yi shahada, da Falasdinawa sama da 50,000, da suka yi shahada a Gaza da jinin Sayyed Hassan Nasrullahi da Sayyed Hashim Safiyyullah da Imad Mughniya da Isma’il Haniyya da Yahaya Al-Sinwar,   cewa za su ci gaba da gwagwarmaya da kalubalantar mamayar mulkin mallakar Amurka har sai ta mika wuya kuma ta mutunta hakkokin al’ummomi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments