Babban Jami’in Hamas Yace Yan Gwagwarmaya Ba Zasu Ajiye Makamansu Ba.

Kungiyar Hamas ta fito fili ta ce duk wani yunkurin kwace makaman yan gwagwarmaya ba zai yi nasara ba, kuma yayi gargadi game da tsoma

Kungiyar Hamas ta fito fili ta ce duk wani yunkurin kwace makaman yan gwagwarmaya ba zai yi nasara ba, kuma yayi gargadi game da tsoma bakin kasashen waje kan harkokin cikin gidan falasdinawa, kana ya bukaci a bada garanti mai karfi a mataki na biyu na yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Isra’ila

A wata tattaunawa da yayi da gidan talbijin din kasar Yamen Osama Hamdan ya jaddada cewa ba zasu taba mika makamansu ga wani karfi daga waje ba, yan gwagwarmayar sun yi watsi da duk wani karfi daga waje da zai kwabe makamansu su ya tafi da shi, abin da makiya suka kasa yi da karfi da yaji, don haka duk wata shawara ta karbe makaman yan gwagwarmaya to ba za  su taba yarda da shi ba,

Yace isra’ila bata aiki da yarjejeniyar da aka cimma, hatta ma da yarjejeniyar kasa da kasa, kana ya yi gargadin cewa ci gaba da killace Gaza da Isra’ila ke yi, rashin bude hanyoyin shiga yankin da kayan agaji wata alamace dake nuna cewa abokan gaba na da niyyar sake kai hare-hare kan yankin Gaza.

Tun bayan cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin Hamas da Isra’ila da Amurka ta jagoranta a ranar 10 ga watan Oktoban shekara ta 2025 , bisa matakin farko na yarjejeniyar isra’ila za ta bude dukkan kokafin shiga Gaza domin bada damar shigar da abinci da sauran kayan agaji, yayin da ita kuma kungiyar Hamas za ta saki dukkan yahudawan da take tsare da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted