Ministan harkokin wajen kasar Iraki Fuad Hussain ya yi gargadi kan yiyuwar sake bullar kungiyar Daesh a kasar Siriya bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Asad.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hussain ya na fadar haka a birnin Riyad na kasar Saudiya inda aka gudanar da taro na musamman kan kasar ta Siriya.
Ministan ya kada da cewa a halin yanzu yankin hamadar ‘Hauran” wanda ya mike har zuwa kan iyaka da kasar Iraki, wato zuwa yammacin lardin Ambar na kasar Iraki, da kuma yankin Kudu masu yammacin lardin Dir’aa na kasar Siriya sun zama wuraren da yan ta’adda suke boyewa, sannan suna iya sulalewa su tsallaka kan iyakar kasashen biyu zuwa cikin kasar Iraki, ba tare da an ganosu ba.
Fuad ya ce korewar da kasar Iraki take da shi a yaki da ta’addanci ya na da matukar muhimmanci don kaucewa wata sabuwar fitina ta Daesh a yankin.
Daga karshe ministan ya kammala da cewa akwai hatsari sosai ga yankin yammacin Asiya idan kungiyar Daesh mai kafirta kowa ta sake bullowa a yankin.