Najeriya : Babban Hafsan Soji Ya Ziyarci Maiduguri Bayan Kisan Sojoji

Kwanaki kadan bayan kashe sojojin tarayyar Nigeria su 15,babban hafsan sojan kasar ya kai ziyarar aiki a Jahar Borno a jiya Lahadi. Majiyar tsaro a

babban hafsan sojan nigeria

Kwanaki kadan bayan kashe sojojin tarayyar Nigeria su 15,babban hafsan sojan kasar ya kai ziyarar aiki a Jahar Borno a jiya Lahadi.

Majiyar tsaro a Borno ta ce masu ikirarin jihadi ne su ka kai hari akan wani sansanin soja tare da kona shi, bayan da su ka kashe sojoji 15 a cikinsa.

Kungiyar Daular Musulunci A Yammacin Afirka ( ISWAP) ce ta kai hari a kauyen Mairari a gabar Ruwan tafkin Chadi a daren talata washe garin laraba.

Majiyar ta ce, maharan sun kone sansanin baki daya.

Bayan sojoji 15 da su ka kashe, maharan sun kuma kashe biyar daga mayakan rundunar fararen hula masu taimakawa jami’an tsaro a a fada da masu dauke da makaman ( JTF).

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ce sansanin sojan ya kone baki daya sanadiyyar harin.

Tuni dai sojojin da su ka saura su ka janye zuwa garin Monguno mai nisan kilo mita 18.

Jahar Borno dai ita ce cibiyar kungiyoyi masu tayar da kafar baya dake danganta kansu da musulunci da su ka hada Boko Haram da kuma Iswap. Tun daga shekarar 2009 ne kungiyar Boko haram take kai hare-hare a cikin sassa mabanbanta na jihar ta Borno wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane da kuma tilastawa wasu miliyoyi yin hijira.

Wani mazaunin garin na Mairari ya ce; An kai harin ne a cikin daren da misalin karfe 11; kuma na yi batakashi da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted