Babban Daraktan Hukumar IAEA, Zai Ziyarci Iran ranar Laraba

Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya  zai ziyarci Tehran a ranar Laraba mai zuwa. Ziyarar ta Grossi na zuwa ne gabanin sabuwar

Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya  zai ziyarci Tehran a ranar Laraba mai zuwa.

Ziyarar ta Grossi na zuwa ne gabanin sabuwar tattaunawar da za’ayi tsakanin Iran da Amurka a ranar Asabar mai zuwa kan batun shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya ce shugaban hukumar ta IAEA Rafael Grossi zai ziyarci Tehran a ranar Laraba.  

Gharibabadi ya bayyana cewa, babban daraktan hukumar ta IAEA, zai gana da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI) Mohammad Eslami.

Ya kara da cewa “ziyarar na cikin tsarin ci gaba da hulda da hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.”

Ziyarar ta shugaban hukumar ta IAEA za ta zo ne a daidai lokacin da Iran da Amurka ke shirin gudanar da tattaunawar ta biyu, wanda Oman ta shiga tsakani a ranar Asabar data gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments