Shugaban Kwamitin Tsaron Kasa da Manufofin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Makomar ‘yan Sahayoniyya halaka ce a hannun jaruman al’ummar Iran da kuma Æ™ungiyoyin ‘yan gwagwarmaya
Shugaban Kwamitin Tsaron Kasa da Manufofin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci (Majalisar Dokoki) ya tabbatar da gazawar sabuwar koyarwar tsaro ta kungiyar ‘yan Sahayoniyya, yana mai cewa, “Wannan koyarwar ba wai kawai ba ta bayar da wata mafita ga wannan kungiyar ba, har ma ba ta ba ta damar tunani mai kyau ba.”
A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran Ibrahim Azizi, shugaban Kwamitin Tsaron Kasa da Manufofin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran {wato Majalisar Dokokin kasa} ya wallafa wani sako a shafinsa na yanar gizo-gizo, yana gargadin ‘yan Sahayoniyya cewa: “Sabuwar koyarwar tsaro ta wannan kungiyar karya ce kawai da mafarki maras tushe kuma mai adawa ya gaza; ba wai kawai ba za ta kai ku zuwa ga wata hanyar ceto ba ce, har ma ba za ta ba ku damar ceton kan ku ba. Saboda babban sakamakonku shi ne halaka a hannun jaruman mutanen Iran da kuma Kungiyoyin gwagwarmaya.”