Shugaban makarantun addinu a nan JMI Aya. Aarafi ya bayyana cewa fahintar addini da kuma akidar Imam Khumaini (q) wanda ya kafa JMI akidace tsayayye kan addinin musulunci na asali a kan Alkur’ani mai girma da tafarkin iyalan gidan manzon All..(s).
Kamfanin dillancin labaran Parstoday ya nakalto Aya. Alireza Aarafi yana fadar haka a lokacinda yake tattaunwa da masana da malaman falsafa a kasar Rasha.
Labarin ya kara da cewa Arafi ya je kasar Rasha ce don halattan taron kasa da kasa ta hanyar kusanci zuwa ga All..ta (Abrisham) ko al-Hariri, tare da gayyatar shugaban majalisar musulmi na kasar Rasah.
Aya. Aarafi ya bayyana cewa, Imam Khomaini (q) wanda ya kafa JMI ya kafata ne bisa asasin ilmantarwan alkur’ani mai girma da kuma koyarwan limamai masu tsari daga iyalan gidan manzon All..(s).
Taron dai ya sami halattar manyan manyan malaman daga akidu da falsafa daga addinai daban daban, inda suka gabatar da jawabai sannan suka yi musanyan ra’ayi dangane da akidun addinai da kuma ra’ayoyin malamai a kansu.Aya. Aarafi Ya Ci Akidar Imam Khomaini (q) Babu Wace Gona Da Iri A cikinsa