Ayatullah Khatami: Jerin Gwanon Ranar Qudus Rana Ce Mai Matukar Muhimmaci A Musulunci

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan Tehran a jiya Juma’a ya bayyana cewa; Jerin gwanon ranar Kudus tana da matukar muhimmanci a addinin musulunci,

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan Tehran a jiya Juma’a ya bayyana cewa; Jerin gwanon ranar Kudus tana da matukar muhimmanci a addinin musulunci, yana mai kara da cewa: Muna godewa Allah madaukakin sarki cewa, ranar kudus ta wannan shekarar ta bunkasa fiye da shekarun baya.”

Haka nan kuma ya kara da cewa; Imam Khumaini ( r.a) da ya ayyana ranar Kudus a duniya a 1979, wacce ita ce juma’ar karshe ta watan Ramadan, a wancan lokacin manyan kasashen duniya masu takama da karfi suna kokarin ganin an mance da batun Falasdinu da kuma kasakantar da shi da cewa batu ne na Larabawa kadai.

Limamin na Tehran ya kuma kara da cewa, abinda Imam Khumain ( r.a) ya yi na ayyana ranar Kudus, wata hikima ce wacce ta dakile makarkashiyar da makiya su ka kitsa.

Ayatullah Khatami ya kuma yi ishara da yadda aka yi jerin gwanon na ranar Kudus a cikin garuruwa da birane 900 a cikin fadin Iran.

A fadin duniya kuwa limamin na Tehran ya yi ishara da cewa an yi jerin gwanon ranar Kudus a cikin kasashe 80 da su ka hada Amurka, Birtaniya, Faransa da kuma Jamus.

Dangane da barazanar da shugaban kasar Amurka yake yi wa Iran, limamin na Tehran ya ce, babu abinda ya iya sai barazana saboda halinsa na tsoro, kuma abin mamaki ne a ce har yanzu bai san cewa, barazanarsa  ba ta da wani tasiri ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments