Ayatollah Khamenei: Ba za a iya murkushe yunkurin Guguwar Al-Aqsa ba

Jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Iran Imam Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa ba za a iya kawar da yunkurin Guguwar Al-Aqsa

Jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Iran Imam Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa ba za a iya kawar da yunkurin Guguwar Al-Aqsa ba, yana mai jaddada cewa haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gushe daga samuwa.

Bayanin na Jagoran, na zuwa ne biyo bayan fara aiwatar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta a yakin da aka yi tsakanin Haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma dakarun Hizbullah na kasar Lebanon.

An fara aiwatar da yarjejeniyar ne tun daga ranar Talata, bisa sharudda na musamman da suka kunshi janyewar dukkanin sojojin Isra’ila daga yankunan da suka kutsa-kai a cikin kauyuka da garuruwan da ke kudancin kasar Lebanon, a yayin da dakarun gwamnatin kasar Lebanon da na majalisar dinkin duniya za su karbi ragamar harkokin tsaro a cikin wadannan yankuna.

A bisa wannan yarjejeniyar dai sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila za su kammala janyewa daga yankunan da suka shiga ne a cikin kwanakin 60, yayin da sojojin Lebanon tuni suka fara isa wadannan yankuna domin fara ayyukansu.

Yarjejeniyar dai ta sami amincewar bangarorin siyasa da dama na kasar ta Lebanon, duk da cewa akwai mutanen da suke ganin cewa da wuya Isra’ila ta kiyaye sharuddan yarjejeniyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments