Au Ta Yi Gargadi Akan Barkewar Sabon Rikici Tsakanin HAbasha Da Eritrea

Kungiyar tarayyar Afirka ta fitar da sanarwa da a ciki ta bayyana cewa tana bibiyar saboda halin dar-dar da ya barke a tsakanin kasashen Habasha,
ZAUREN TARON AFIRKA

Kungiyar tarayyar Afirka ta fitar da sanarwa da a ciki ta bayyana cewa tana bibiyar saboda halin dar-dar da ya barke a tsakanin kasashen Habasha, Eritrea da kuma Masar.

Sanarwar da kungiyar tarayyar ta Afirka ta fitar a jiya Alhamis ta yi kira ga kasashen uku da su kai zuciya nesa da kuma kaucewa daukar duk wani mataki ko yin wani furuci wanda zai kara ruruta wutar rashin jituwar dake tsakaninsu.

Tarayyar Afirkan ta yi kira da a yi amfani da hanyoyin diplomasiyya a tsakanin kasashen uku domin warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tataunawa, da hakan yake a matsayin daya daga cikin dokokin kafuwar tarayyar Afirka.

Haka nan kuma tarayyar Afirkan ta bayyana kasantuwarta cikin shiri domin hada kasashen uku su tattauna saboda rage zafin sabanin dake tsakaninsu.

Yankin zirin Afirka da gabar Ruwan Maliya yana fuskantar sabani a tsakanin muhimman kasashen yankin da su ne HAbasha, Eritrea da kuma Kasar Masar da yake da tushe na tarihi, sabanin iyakokin kasa da kuma siyasa.

KAsashe Habasha da Eritrea sun yi fada da juna a tsakanin 1998 uzwa 2000 wanda ya ci rayukan dubban mutane. Kum duk da cewa sun rattaba  hannu akan yarjejeniyar Algeria a 2000 sabanin a tsakanin wadannan kasashen biyu bai zagwanye ba. Ita kuwa kasar Masar tana da sabani ne da Habasha akan madatsar Ruwan da Addis Ababa ta gina wanda yake rage yawan Ruwan Maliya da yake shiga Masar. Wannan sabanin, ya sa Alkahira da Asmara sun karanci juna a wani da ake ganin hade baki domin kalubalantar Habasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted