AU ta dakatar da Guinea-Bissau daga zama mamba a cikinta bayan juyin mulkin sojoji

Kungiyar Tarayyar Afirka, AU ta sanar da dakatar da kasar Guinea-Bissau daga zama mamba a kungiyar bayan hambarar da shugaban kasar, Umaro Sissico-Embalo da sojoji

Kungiyar Tarayyar Afirka, AU ta sanar da dakatar da kasar Guinea-Bissau daga zama mamba a kungiyar bayan hambarar da shugaban kasar, Umaro Sissico-Embalo da sojoji suka yi.

Shugaban Kungiyar Mahamoud Youssouf ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na AFP.

Matakin na AU na zuwa ne sa’o’i bayan kungiyar ECOWAS, ta dakatar da kasar saboda juyin mulkin.

Ecowas ta ɗauki matakin dakatar da ƙasar ne a wani taro da ta gudanar a ranar Alhamis.

Sojoji sun yi juyin mulki a kasar ne yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasar.

Tunda farko dama Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da ya faru a ranar Alhamis a kasar Guniea Bissau, kwanaki uku bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, inda ta kira shi da “barazana kai tsaye ga zaman lafiyar kasar da yankin.”

Wannan “juyin mulkin soja” ya zama “mummunan keta tsarin mulki” kuma “barazana kai tsaye ne ga zaman lafiyar kasar da yankin baki daya,” in ji ECOWAS a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments