AU, Ta Bukaci Da A Gaggauta Dakatar Da Fada A Gabashin DR Congo

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi kira da a gaggauta dakatar da fadan da ya kara kamari a ‘yan makonnin nan a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi kira da a gaggauta dakatar da fadan da ya kara kamari a ‘yan makonnin nan a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC).

 Shugaban Hukumar AU, Moussa Faki Mahamat, “ya yi kira da a kiyaye tsagaita bude wuta da aka cimma a tsakanin bangarorin da kuma dakatar da duk wani tashin hankali cikin gaggawa” sannan “ya yi kira ga bangarorin da su kiyaye rayukan fararen hula,” a wata sanarwa da ya fitar.

Akalla dakarun wanzar da zaman lafiya 12 ne aka kashe a fadan da ake a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongon.

Daga cikinsu akwai sojojin Afirka ta Kudu tara da uku na Malawi, kamar yadda hukumomi suka sanar.

Rikicin mai nasaba da kungiyar ‘yan tawayen M23 da aka kwashe shekaru uku ana yi a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango mai arzikin ma’adinai ya tsananta a cikin watan Janairu inda ‘yan tawayen suka karbe iko da wasu yankuna, lamarin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin yiwuwar barkewar yakin basasa.

M23 dai na daya daga cikin kungiyoyin masu dauke da makamai kusan 100 da ke fafutukar ganin sun samu gindin zama a gabashin DRC mai arzikin ma’adinai, daura da kan iyaka da kasar Rwanda, wanda ya haifar da daya daga cikin manyan matsalolin jin kai a duniya.

Tun daga 1998, kusan mutane miliyan shida ne aka kashe yayin da kusan miliyan bakwai suka yi gudun hijira a cikin gida.

Sama da mutane 237,000 ne fadan da ake gwabzawa a gabashin Kongo ya raba da muhallansu tun daga farkon wannan shekara, inji hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD a makon jiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments