Cibiyar CDC Na Afirka Da WHO Suna Aiki Tare Don Kawo Karshen Cholera
Cibiyar Africa Centres for Disease Control and Prevention (Africa CDC) da kuma hukumar lafiya ta Dunita (WHO) sun hada kai don ganin an kawo karshen cutar colera a nahiyar ta Afirk, tare da hada kai da kasashen Nahiyar.
Kamfanin yana labarai ta interner Afriva News ya bayyana a ranar Jumma’a kan cewa, shirin wanda yake cikin shirye-shiryen kiwon lafiya na cibiyar Afrika CDC na shekara ta 2025-2026. Sannan manufar shirin itace rage cutar ta Colera da kasha 90 a wannan shekarar, sannan kawo karshen cutar kwata-kwata a kashe 20 na nahiyar nan da shekaru 2030.
Cutar colera dai tana kama mutane ne ne saboda shan ruwa marasa tsabta, da kuma abinci marasa tsabta.
Cutar tafi kashe mutane a nahiyar Afirka a ko wace shekara, kuma a wannan karon zasu yi amfani da alluran riga kafi na cutar ga yara kanana, sannan da hanyoyin tsabta da kiwon lafiya mai kyau.
Tarayyar Najeriya dai daga daga cikin kasashen da suka fi fama da wannan cutar, kan sauran kasashen Afrika.