ASUU: Gwamnatin Najeriya ba ta aiwatar da ko daya daga cikin bukatunmu ba

Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), Farfesa Chris Piwuna, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta aiwatar da ɗaya daga cikin yarjejeniyar da ta ƙulla

Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), Farfesa Chris Piwuna, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta aiwatar da ɗaya daga cikin yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙungiyar ba.

Farfesa Piwuna, ya ce ASUU a koyaushe na zaɓar tattaunawa da jami’an gwamnati a matsayin mafita.

Amma duk da cewa sun cimma matsaya kan batutuwa masu muhimmanci kamar kuɗaɗen gudanarwa, albashi, ’yancin malamai, ‘yancin jami’o’i, da sake duba wasu dokoki, ba a ɗauki mataki kan kowanne ba.

“Babu saɓani a tsakaninmu da tawagar gwamnati,” in ji shi.

“Mun amince kan abubuwa da dama, sai dai shugabanninsu, Ma’aikatar Ilimi da Gwamnatin Tarayya ba su ɗauki mataki kan kowanne ba.”

Ya danganta yawan ficewa daga Najeriya da malamai da likitoci ke yi saboda ƙarancin albashi da mummunan yanayi da suke ciki.

A asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos inda yake aiki, ya ce aƙalla likitoci 20 sun bar aiki cikin shekara biyu.

“Yanayin daidai yake da na malaman jami’a. Idan ƙarancin albashi ne ke sa mutane barin aiki, me ya sa ba za a ƙara albashi a riƙe su ba?” ya tambaya.

Ya ƙara da cewa ƙasashe da dama a Afirka suna ɗaukar malaman Najeriya aiki.

“A Uganda, a cikin jami’a guda ɗaya za ka iya samun malamai ’yan Najeriya sun kai 20,” in ji shi.

Shugaban ASUU ya kuma nuna damuwa kan mummunan yanayin kayan aiki a jami’o’in Najeriya, inda ya ce hakan na daga cikin dalilan da ya sa ba sa samun matsayi mai kyau a duniya.

Ya ce daga cikin jami’o’i 333 da faɗin Najeriya, guda biyar ne kaɗai ke cikin jirin manyan jami’o’i 1,000 a nahiyar Afirka.

Ya ce malamai ba sa jin daɗin tafiya yajin aiki, amma gwamnati na tilasta musu hakan saboda rashin ɗaukar mataki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments