Asusun Unicef Ya Yi Tir Da Kashe Kananan Yara 35 A Kurdufan Na Kasar Sudan

Asusun kananan yara na MDD ya fitar da sanarwa a jiya Talata da a ciki ya yi tir da kai harin daya yi sanadiyyar kashe

Asusun kananan yara na MDD ya fitar da sanarwa a jiya Talata da a ciki ya yi tir da kai harin daya yi sanadiyyar kashe kananan yara 35 a Jahar Kurdufan ta Arewa a kasar Sudan.

Manajar zartarwa ta asusun kananan yaran na MDD Katherin Russel ta bayyana cewa;  Da akwai firgitarwa a cikin rahotannin da suke nuni da cewa an kashe fararen hula 450 da jikkata 24 da mata 2 masu ciki a wani mummunan hari a kusa da garin Bara.

Haka nan kuma ta ce harin dai an kai shi ne akan garuruwan “shaqqul-Nu’am” da “Hillatu -Hamid” da suke a Jahar Kurdufan ta arewa a karshen makon da ya shude.

Asusun na MDD ya kuma nuna damuwa akan yiyuwar a sami karuwar adadin yaran da za su rasa rayukansu bisa la’akari da raunuka masu hatsari da su ka samu.

Katherine ta zargi masu kai harin da cewa suna wasa da rayuwar bil’adama da daukarta ba wani abu ba, da hakan keta dokokin kasa da kasa ne.

A cikin makwannin bayan nan dai an sami karuwar tashe-tashen hankula a cikin yankin na Kurdufan ta Arewa , da hakan ya yi sanadiyyar yin hijirar mazauna yankin zuwa inda za su sami aminci.

Haka nan kuma ta ce bai kamata a rika barin masu aikata laifuka irin waddan suna tsallakewa fuskantar sharia ba,musamman idan lamarin ya shafi rayuwar kananan yara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments