Arif: A Shirye Muke Mu Sabunta Sana’o’in Sudan

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Ridha Arif ya bayyana cewa; Da akwai bukatar fadada da bunkasa alakar dake tsakanin Iran da Sudan, sannan

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Ridha Arif ya bayyana cewa; Da akwai bukatar fadada da bunkasa alakar dake tsakanin Iran da Sudan, sannan ya kara da cewa; Iran din a shirye take ta yi aiki da Sudan domin bunkasa sana’o’inta.

Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya furta haka ne dai a lokacin da ya gana da ministar masana’antu ta Sudan Mahasin Ali Yakub da ta kawo Ziyara Iran.

Muhammad Ridha Arif ya yi wa Sudan fatan alheri da son ganin zaman lafiya ya dawo, sannan kuma ya bayyana sake bude ofishin jakadancin Sudan a Tehran a shekarar da ta gabata a matsayin alamar kyautatuwar alaka a tsakanin kasashen biyu.

Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya zargi kasashen turai da kuma HKI da haddasa fitintinu da rarraba a cikin kasashen musulmi da kuma karkatsasu zuwa kananan kasashe. Sai dai ya bayyana cewa da yardar Allah kasashen na turai ba za su yi nasara ba.

A nata gefen, ministar masana’antu ta kasar Sudan din  ta bayyana tausayawa ga gwamnati da kuma al’ummar Iran akan hatsarin da ya faru a tashar jiragen ruwa ta Shahid Raja’i dake kudancin Iran wacce daruruwan mutane su ka rasa rayukansu da kuma jikkata.

Ministar ta kasr Sudan ta bayyana Jamhuriyar musulunci ta Iran a matsayin babbar kasa wacce ta ci gaba, kuma Sudan tana da bukatuwa da ci gaban da ta yi a cikin fagage mabanbanta na kere-kere.

Ministar ta kasar Sudan  Mahasin  Ali Yakub, ta bayyana fatan ganin Iran ta taimaka wajen sake gina Sudan da ta fuskanci rushewar cibiyoyinta da dama saboda yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments