Araqci: Iran Ba Za Ta Daina Taimakawa Kungiyoyin Gwagwarmaya Ba

A hirar da tashar  talbijin din ‘aljazira’ ta yi da shi, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqci, ya bayyana cewa; Iran ba za ta daina

A hirar da tashar  talbijin din ‘aljazira’ ta yi da shi, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqci, ya bayyana cewa; Iran ba za ta daina taimakwa kungiyoyin gwgawarmaya ba, tare da cewa, Iran ba ta son yaki,amma a lokaci daya a shirye take ta fuskanci duk abinda zai faru.

Da yake Magana akan yiyuwar Isra’ila za ta kawo wa Iran hari, ministan harkokin wajen Iran din ya ce; Isra’ilawa za su iya gwada azamar Iran su gani, za su  fahimci girman martanin da za ta mayar.

Ministan harkokin wajen Iran din ya kuma ce; Kungiyoyin gwagwarmaya suna da karfi da za su iya mayarwa da ‘yan sahayoniya martani, kuma taimakon da muke ba su ba zai takaita a cikin harkokin siyasa da diplomasiyya kadai ba, za mu yi duk abinda ya dace.

Da yake Magana akan ziyarar da ya kai zuwa kasar Lebanon, Abbas Araqci ya ce, mun yi tattaunawa mai matukar muhimmanci,matsayinmu shi ne muna goyon bayanmu ga  dukkanin matakin da gwamnati da kuma ‘yan gwgawarmaya za su dauka.

 Da ya amabci ziyararsa zuwa kasar Saudiyya da Qatar kuwa, ministan harkokin wajen na Iran ya yi ishara da yadda kowance daya daga cikinsu take taka  rawa a cikin wannan yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments