Araqchi Ya Tattauna Da Takwarorinsa Na Rasha Da Pakistan

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya tattauna mafi mahimmancin batu da takwarorinsa na Rasha da Pakistan Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tattaunawa

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya tattauna mafi mahimmancin batu da takwarorinsa na Rasha da Pakistan

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov da kuma na Pakistan Mohammad Is’haq Dar game da sabbin abubuwan da suka faru a yankin.

A cikin tattaunawarsa da takwaransa na Rasha Lavrov, Araqchi ya yi masa bayani game da matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran game da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta yi, ciki har da toshe hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar ruwa ta Hormuz ba bisa ka’ida ba da kuma kwace jirgin ruwan Iran mai dauke da kayan agaji.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta jaddada cewa: Moscow ta jaddada muhimmancin ci gaba da kokarin diflomasiyya don hana karuwar tabarbarewan al’amura tsakanin Iran da Amurka da kuma guje wa duk wani rikici da ba a so.

Ministan Harkokin Wajen Iran ya kuma yi tattaunawa ta wayar tarho da Ministan Harkokin Wajen Pakistan, inda suka yi nazari kan sabbin abubuwan da suka faru a yankin da kuma batutuwan da suka shafi tsagaita wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted