Araqchi Ya Mayar Da Martani Ga Furucin Shugaban Amurka Trump

Ministan harkokin wajen Iran ya mayar da martani ga shugaban Amurka kan mamakin dalilin da yasa Iran ba ta mika wuya ba? Ministan Harkokin Wajen

Ministan harkokin wajen Iran ya mayar da martani ga shugaban Amurka kan mamakin dalilin da yasa Iran ba ta mika wuya ba?

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya amsa tambayar shugaban Amurka game da dalilin da yasa Iran ba ta mika wuya ba, yana mai cewa: “Domin su ‘yan Iran ne.”

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya amsa tambayar shugaban Amurka game da dalilin da yasa Iran ba ta mika wuya ba duk da matsin lambar Amurka da tarin sojoji da nufin tilasta wa Iran shiga yarjejeniya kan sharuddan Amurka.

Ya ce: “Kana tambaya me yasa Iran ba ta mika wuya ba? Domin su ‘yan Iran ne.”

Wakilin Trump, Steve Witkopf, ya ce a wata hira da Fox News cewa: Trump yana matsa lamba ga bangaren Iran a lokacin tattaunawar makamashin nukiliya, yana mai cewa: Trump ya yi mamakin kin amincewa da Iraniyawa na mika wuya ga matsin lamba da kuma kasancewar sojojin Amurka da aka tura zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya nuna a ranar Lahadi cewa: Tawagar Iran za ta gana da bangaren Amurka ranar Alhamis mai zuwa a Geneva, yana mai jaddada cewa: Cimma yarjejeniya da Amurka tana nan daram kuma yana tabbatar da cewa akwai fannoni da zasu iya fin yarjejeniyar shekara ta 2015 kyau.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted