Araqchi Ya Karbi Sakon Ta’aziyya Daga Saudiyya Da Pakistan

Ministan Harkokin Wajen Iran ya tattauna da takwaransa na Saudiyya da kuma Fira Ministan Pakistan ta hanyar wayar tarho Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Faisal bin

Ministan Harkokin Wajen Iran ya tattauna da takwaransa na Saudiyya da kuma Fira Ministan Pakistan ta hanyar wayar tarho

Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Faisal bin Farhan ya mika ta’aziyya ga Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi bisa rasuwar ‘yar uwarsa, Malama Badr Al-Sadat Araqchi.

Firayim Ministan Pakistan Shahbaz Sharif shi ma ya kira Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ta wayar tarho don nuna ta’aziyyarsa kan rasuwar ‘yar uwarsa, yana addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya yi mata rahama da gafara da kuma gadar da haƙuri da ta’aziyya ga iyalanta.

Araqchi ya gode wa Fira Ministan Pakistan saboda ta’aziyya da jaje da ya yi masa a wannan lokaci mai zafi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted