Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya isa kasar tunisiya domin tattaunawa da hukumomin kasar, a ci gaba da ziyarar da yake yi a yammacin Afrika, bayan da ya bar kasar masar inda ya gana da directan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya kuma suka cimma matsaya tsakaninsu,
An tsara cewa babban jami’in diplomasiyar na iran zai gana da ministan harkokin wajen kasar inda za su tattauna game da dangantar dake tsakanin kasashensu, da ma na kasa da kasa,
A wani sako da ya aike da shi a shafin sa na X Araqchi ya nuna jin dadinsa sosai da kuma jinjinawa ga gwamnatin kasar masar game da rawar da ta taka a bangaren diplomasiya a tattaunawasu da hukumar IAEA.
Ya kara da cewa nasarar da aka samu ta samu ne da kokarin ministan harkokin wajen masar da kuma shugaban kasar Ibrahim sisi, yana mai cewa al’ummar Iran na daukar kansu a matsayin aboki ga duk wata al’ummar da ta fifita zaman lafiya a kan rikici da tashin hankali.