Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana Taron Tsaro na Munich a matsayin “Munich circus,” inda ya soki manufofin Tarayyar Turai da wasu ƙasashen Turai game da Tehran.
Araghchi ya rubuta a shafin sada zumunta na X na kamfanin Amurka a ranar Asabar cewa, “Abin takaici ne ganin yadda Taron Tsaro na Munich, wanda aka saba da muhimmancinsa, ya koma ‘Munich Circus’ idan batun Iran ya taso.”
Ya ce wannan koma-baya, inda aka fifita kwaikwayo kan ainihin batutuwa, yana ɗauke da muhimman saƙonni, yana mai cewa Tarayyar Turai tana “cikin ruɗani, sakamakon gazawarta wajen fahimtar abin da ke faruwa a cikin Iran.”
“Ta fuskar dabarun siyasa, Tarayyar Turai mara manufa ta rasa duk wani tasiri na siyasa a yankinmu,” in ji Araghchi.
Ya ware Jamus da suka ta musamman, yana cewa Berlin “ita ce ke jagorantar miƙa manufofinta na yankin gaba ɗaya ga Isra’ila.”
Araghchi ya bayyana alkiblar Turai gaba ɗaya a matsayin “mai muni,” yana ƙara da cewa “gurguncewa da rashin tasirin Tarayyar Turai/E3 (Birtaniya, Faransa da Jamus) ya bayyana a yadda tattaunawar da ake yi kan shirin nukiliyar Iran ke gudana.”
“Da a baya Turai ta kasance muhimmin mai shiga tsakani, amma yanzu babu ita babu labari,” in ji shi.
A maimakon haka, Araghchi ya ce abokan hulɗar Iran a yankin sun zama “masu tasiri da taimako fiye da E3 mara ƙarfi kuma a gefe.”
Ba a gayyaci Iran zuwa taron na bana ba. Masu shirya taron sun ce ba wannan ne lokacin da ya dace a shiga mu’amala da Tehran ba, sakamakon murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnati a baya-bayan nan.
Sai dai taron ya karɓi Reza Pahlavi, ɗan tsohon Shah na Iran, Mohammad Reza Pahlavi, tare da ba shi damar gabatar da jawabi inda ya yi kira ga Amurka da Isra’ila su tsoma baki kan Iran.
Birnin Munich na Jamus ne ke karɓar bakuncin bugu na 62 na Taron Tsaro na Munich na tsawon kwanaki uku, wanda ya fara a ranar Juma’a, ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro da tsari, la’akari da yanayin siyasar duniya a halin yanzu.
A ranar 29 ga Satumba, Tarayyar Turai ta sake kakaba takunkuman da suka shafi shirin nukiliya kan Iran ta hanyar tsarin “snapback” da ke da alaƙa da yarjejeniyar nukiliya ta 2015.
Matakin ya dawo da jerin takunkumai da dama da aka ɗage ko dakatar a ƙarƙashin Yarjejeniyar Shirin Hadin Gwiwa na Nukiliya (JCPOA), ciki har da takunkumi kan banki, makamashi, sufuri na ruwa, inshora da ciniki da kayayyaki masu muhimmanci.
Tehran ta ƙi amincewa da halaccin matakin, tana mai cewa ɓangarorin da suka fice ko suka karya yarjejeniyar nukiliya ba su da hurumin kiran tsarin “snapback,” tare da gargadin cewa matakin zai ƙara raunana ƙoƙarin diflomasiyya.