Araqchi Ya Bayyana Makomar Sinadarin Uranium Da Iran Ta Inganta A Lokacin Yaki

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana makomar sinadarin uranium da Iran ta tace bayan harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyarta Ministan harkokin

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana makomar sinadarin uranium da Iran ta tace bayan harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyarta

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa, har yanzu ba a warware makomar sinadarin uranium da aka inganta da ya kai kashi 60 cikin 100 ba, yana mai cewa an adana kayayyakin a cibiyoyin makamashin nukiliyar da aka kai harin.

A wata hira da jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya, Araqchi ya ce har yanzu ana ci gaba da tantance barnar da aka yi a cibiyoyin makamashin nukiliyar, kuma samun damar shiga wasu wuraren da abin ya shafa na da matukar wahala, lamarin da ya sa ba a san makomar uranium sama da kilogiram 400 ba.

Dangane da tambayar ko an cire muhimman kayan aikin cibiyoyin kafin a kai harin? Araqchi ya amsa da cewa: “Ya aike da wasika zuwa ga Grossi (Daraktan Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya) cewa Suna iya daukar matakan kare kayayyakin cibiyoyin makamshin nukiliyarsu, amma a zahiri bai ce sun cire su ba.

Ya yi nuni da cewa: Uranium din akwai yiwuwar ya samu matsala ko kuma an tarwatsa shi, amma har yanzu ba a kammala tantancewar karshenmakamarsa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted