Araqchi: Tattaunawar Muscat Diflomasiyya Ce Ba Batun Mika Kai Ba

Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Tattaunawar Muscat Diflomasiyya ce ba tare da sassauci ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana yanayin

Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Tattaunawar Muscat Diflomasiyya ce ba tare da sassauci ba

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana yanayin tattaunawar da ta gudanar a birnin Muscat na kasar Oman da cewa; Ta yi kyau kuma an cimma matsaya kan ci gaba da tattaunawar.

Ministan harkokin wajen Oman Badr Al-Busaidi ya jaddada cewa: Tattaunawar da aka yi tsakanin Iran da Amurka ta taimaka wajen fayyace ra’ayoyin ɓangarorin biyu.

A nashi ra’ayin shugaban Amurka Donald Trump ya ce: Tattaunawar ta yi kyau sosai, kuma da alama Iran tana da sha’awar cimma yarjejeniya.

Yayin da Fadar White House ta Amurka ta jaddada cewa: Tattaunawar ta buɗe ƙofa ga ci gaba da muhimmiyar hanyar diflomasiyya duk da ƙalubalen amincewa tsakanin ɓangarorin biyu.

A gefe guda kuma, Majalisar Haɗin Gwiwar kasashen Larabawan Tekun Pasha ta bayyana cewa: Tattaunawar mataki ne mai kyau don rage tashin hankali a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted