Araqchi: Ta Hanyar Tattaunawa Ce Kawai Za’a Iya Warware Matsalar Cikin Gida

Ministan harkokin wajen kasar Iran abbas Araqchi  da takwaransa na kasar Oman badar abu said sun gana a birnin Tehran a wata ziyara da ya

Ministan harkokin wajen kasar Iran abbas Araqchi  da takwaransa na kasar Oman badar abu said sun gana a birnin Tehran a wata ziyara da ya kawo kasar iran ajiya Asabar, kuma ya gana da manyan jami’an gwamntin kasar wanda haka ke nuna irin kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Ministocin guda biyu sun yi taron manema labarai kuma ministan harkokin wajen iran ya yi ishara game da alaka mai karfi dake tsakanin kasashen biyu mai cike da tarihi da ma alaadu, kuma sun yi musayar ra’ayi tsakani a bangarori daban-daban da kasashen za su ci gajiyar juna, musamman kan yarjeniyoyi da aka cimma a lokacin ziyarar shugaban kasar a iran.

Haka zalika ministan harkokin wajen iran ya fadi cewa ganawar ta su ta jaddada matsayin kasashen biyu na yin aiki tare wajen tabbatar da tsaro da zama lafiya a yankin tekun fasha, kana sun bukaci a kawo karshen kisan kare dangi da isra’ila ke yi wa alummar gaza

,kuma sun bukaci tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a kasar Yamen, kuma sun nuna cewa ashirye suke su bada gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin dukkan bangarorin kasar Yamen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted