Araqchi: Manufofin Amurka Sun Kasa Cimma Nasara Kan Iran

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Ba a cimma mummunan burin ƙarya Iran ba har ta kai ga miƙa wuya ba tare da sharaɗi

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Ba a cimma mummunan burin ƙarya Iran ba har ta kai ga miƙa wuya ba tare da sharaɗi ba

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Mika wuyan Iran ba tare da wani sharaɗi ba ruɗani ne na ƙarya wanda bai taɓa faruwa ba.

A cikin wata sanarwa, Araqchi ya lura cewa a farkon yaƙin, Shugaban Amurka Donald Trump ya faɗi a taƙaice, “Miƙa wuya ba tare da sharaɗi ba.” Wannan yana nufin manufarsu ita ce mika wuyan Iran ba tare da sharaɗi ba, amma Iran ba ta yi hakan ba. Lokacin da suka fahimci cewa wannan mafarkin ba zai yiwu ba, sai suka yi ƙoƙarin rusa gwamnatin kasar; duk da haka, ƙoƙarinsu ya gaza. Sai suka yi ƙoƙarin raba Iran da kuma ba da makamai ga ƙungiyoyi daban-daban a biranen da yankunan yammacin ƙasar, sun yi furuci cewa sun samar musu da makamai, amma sun gaza a wannan ma.

Araqchi ya jaddada cewa; waɗanda suka yi ƙoƙarin tilasta wa Iran mika wuya ba tare da sharaɗi ba, sun roƙi tattaunawa jim kaɗan bayan fara yaƙin. Iran ce ta ƙi tsagaita wuta ta kuma ci gaba da yaƙin har sai sun amince da tsagaita wuta da tattaunawa bisa sharuɗɗan Iran. Za a rubuta waɗannan abubuwan a tarihi. Sun gabatar da shawara mai ma’ana da yawa, kuma Iran ta gabatar da wasu shawarwarin na daban. Sannan suka sake gyara shawararsu, kuma Iran ta sake gyara nata. A ƙarshe, sun amince su yi shawarwari bisa shawarar Iran. Sannan Iran ta amince da tsagaita wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted