Araqchi: Jakadan Australia a Tehran dan koren Isra’ila ne

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi Allah-wadai da matakin da Australia ta dauka na korar jakadan Tehran daga kasar saboda zarge-zargen da

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi Allah-wadai da matakin da Australia ta dauka na korar jakadan Tehran daga kasar saboda zarge-zargen da ake yi na kai hari kan wuraren yahudawa a cikin kasarta, yana mai bayyana hakan a matsayin wani shiryayyen aiki da ake nufin cimma wata manufa ta siyasa da shi.

A cikin wani rubutu a dandalin X ya rubuta cewa,  “Iran na daya daga cikin tsofaffin al’ummomi na duniya, cikin al’ummar Iran  har da yahudawa, saboda haka zargin Iran da kai hare-hare irin wadannan wuraren yahudawa Australia, yayin da muke basu kariya a cikin kasarmu zargi ne maras ma’ana,” in ji shi.

Araghchi ya kara da cewa, Iran na fuskantar wadanann zarge-zarge ne daga gwamnatin Australia saboda matsayarta a kan batun Falastinu, da kuma nuna Rashin amincewa da kisan kiyashin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke yi a kan mata da kananan yara a Gaza.

A jiya Talata, Firayim Ministan Australia Anthony Albanese ya zargi Iran da kitsa hare-hare biyu kan wuraren Yahudawa a cikin watannin Oktoba da Disamba, zargin da aka yi ba tare da gabatar da wata hujja kan hakan ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments