Araqchi: Iran Ta Gabatar Da Shawarwari Ga Masu Shiga Tsakani

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Sun gabatar da yanayi da ra’ayoyi ga masu shiga tsakani a cikin tsari mai inganci da za a

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Sun gabatar da yanayi da ra’ayoyi ga masu shiga tsakani a cikin tsari mai inganci da za a iya aiwatarwa

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Tawagar Iran da ke New York, bisa umarnin da hukumomin da abin ya shafa suka bayar, ta gabatar wa masu shiga tsakani sharudda da ra’ayoyin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin tsarin wani shiri mai inganci da za a iya aiwatarwa.

A matsayin wani bangare na ci gaba da tattaunawa tsakanin Majalisar Shawarar Musulunci (wato Majalisar Dokokin Iran) da Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar kan batutuwa daban-daban na manufofin kasashen waje, an yi taro da Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi da wasu membobin Majalisar Shawarar ta Musulunci.

A lokacin taron, wanda Ali Baba’i Karnami, Shugaban Kwamitin Harkokin Jama’a da wasu membobin Majalisar Shawarar ta Musulunci suka halarta, Ministan Harkokin Wajen ya gabatar da cikakken rahoto kan tattaunawa da ayyukan da suka gudana a lokacin ziyarar tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa New York don halartar zaman Majalisar Dinkin Duniya karo na 81.

Ministan Harkokin Waje ya yi tsokaci kan shawarwari da dama da shi da Shugaban Kasa suka yi da kasashe daban-daban da suka halarci tarukan Majalisar Dinkin Duniya, yana mai jaddada cewa tawagar Iran, bisa dogaro da juriya da jarumtakar al’ummar kasar sun nuna hare-haren soji da makiyansu suka kai musu, ta gabatar da matsayin Iran a fili da kuma karfinta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted