Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar cewa tattaunawa zagaye ta biyu da aka yi ba ta kai tsaye ba da Amurka kan batun cire mata takunkumi an cimma yarjejeniyar kan wasu ka’idoji da za su jagoranci wadanda za su daidaita tattauna ta gaba don cimma yarjejeniya mai karfi.
Da yake hira da manema labarai a ganeva jin kadan bayan kammala tattaunawar Araqchi ya bayyana cewa tattaunawar ta gaske ce, kuma tafi ma’ana fiye da wadda aka yi a baya, kuma an gabatar da shawarwari daban daban da aka yi nazari akan su sosai.
Yace daga karshe dai an iya cimma yarjejeniya kan wasu ginshikai wadanda za’a doru a kansu don ci gaba da tattaunawa don cimma yarjejeniya mai ma’ana.
sai dai da aka tambaye shi game da lokacin da za’a yi tattaunawa ta gaba ya fadi cewa babu wani lokaci da aka sanya, dukkan bangarorin biyu sun amince su yi aiki kan bukatunsu domin kulla yarjejeniya mai karfi, kuma za’a yi musayarsu kafin a sanya lokacin da za a sake zama domin ci gaba da tattaunawar .
Kuma tattaunawar tsakanin iran da Amurka ta gudana ne a gidan jakadan kasar Oman a ganeva kuma an kwashe tsawon sao’I 3 ana yi .