Araqchi; Amurka Ba Ta Gabatar Da Shawarar Rage Sarrafa Yuranium Daga Iran Ba  

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Bangaren Amurka bai gabatar da shawarar rage sinadarin yuranium da Iran ke sarrafawa ba Ministan Harkokin Wajen Iran

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Bangaren Amurka bai gabatar da shawarar rage sinadarin yuranium da Iran ke sarrafawa ba

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Iran ba ta gabatar da wani kuduri na dakatar da tace sinadarin yuranium ba, kuma bangaren Amurka bai nemi “dakatar da tace sinadarin gaba daya ba.”

A wata hira da MSNBC, Araqchi ya jaddada wani batu cewa: Babu mafita ta soja ga shirin makamashin nukiliyar Iran. Ya bayyana cewa an taba gwada wannan batu a baya, cewa an kai hare-hare masu yawa a cibiyoyin Iran kuma an kashe masana kimiyyarta, amma sun kasa lalata shirin makamashin nukiliyar Iran. Ya yi tambaya dalilin da yasa Iran da masana kimiyyarta suka samar da wannan shirin.

Ya kara da fayyace cewa: Wannan fasaha ta Iran ce kuma ba za a iya lalata ta ba ta hanyar jefa bama-bamai ko daukar matakin soja ba. Ya yi ikirarin cewa: Mafita daya tilo ita ce diflomasiyya, shi ya sa Amurka ta koma teburin tattaunawa kuma tana neman kulla yarjejeniya. Ya tabbata cewa: Iran a shirye take don zaman lafiya, a shirye take don diflomasiyya, kuma a shirye take ta kare kanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted