Ministan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Abbas Arakci ya fada wa Fira ministan haramtacciyar Kasar Isra’ila cewa, Iraniyawa suna dakonsa.
Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne a matsayin mayar da martani ga Fira ministan na haramtacciyar Kasar Isra’ila, wanda kotun duniya take nema bisa laifukan yaki,bisa maganganun da ya yi akan Iran da kada kugen yaki da yake yi.
Ministan harkokin wajen na Iran Dr.Arakci ya kara da cewa; yanzu Iran ta kara karfi fiye da lokacin baya, idan kuma kana son gwada sa’a ne to bisimillah. Kuma inda aikinta da mu bai kare ba, to mu ma muna da aiki a tare da kai bai kare ba.
Har ila yau Abbas Arakci ya ce; Netanyahu yana gujea shiga kurkuku ne ta hanyar yi wa Amurka ingiza mai kantu ruwa ta sake shiga wani sabon yakin.