Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya fada a yau Laraba cewa; Duk wata tattaunawar diplomasiyya a karkashin barazar soja, ba za ta haifar da Da,mai ido ba, yana mai kara da cewa; Tattaunawa da Amurka ya kamata ta zama an yi ta ne bisa girmama juna nesa da shifta da kuma barazana ta soja.”
Arakci wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron majalisar ministoci ya kuma ce; Ko kadan, Iran ba ta sami gayyatar tattaunawa ba daga Amurka,” sannan kuma ya ce; Barazanar da Amurkan take yi, da kuma aikewa da sojoji ba zai taba maye gurbin tattaunawa ta gaske ba.”
Sai dai ya yi Ishara da cewa da akwai tattaunawa a tsakani Iran da wasu kasashen larabawa da suke a matsayin masu shiga tsakani, sannan ya ce, mafi yawancin kasashen wannan yankin suna nuna adawa da duk wani hari na soja akan Iran, domin zai hargitsa zaman lafiyar wannan yankin.”
Arakci ya kuma ce;wasu daga cikin wadannan kasashen na yanki, sun nuna cewa a shirye suke da su zama masu shiga tsakanin Iran da Washington, amma babu yadda za a yi tattaunawa ta sami nasara a karkashin barazana da muka matsin lamba wanda babu hankali a cikinsa.”