Arakci:  Babu Batun Tattaunawa Akan Makaman Kasar Iran

Ministan harkokin wajen JMI Abbas Arakci ya bayyana cewa: ” Iran za ta ci gaba da riko da Karfin makaman da Iran take da shi,

ministan harkokin wajen Iran

Ministan harkokin wajen JMI Abbas Arakci ya bayyana cewa: ” Iran za ta ci gaba da riko da Karfin makaman da Iran take da shi, babu kuma wata tattaunawa da za a yi a kansa.”

Arakci wanda ya gana da jakadun kasashen waje da suke a nan Iran ya fada a jiya Asabar cewa; Ina yin godiya ga dukkanin kasashen da su ka yi tir da harin wuce gona da iri akan Iran,musamman akan cibiyoyinta na Nukiliya, su ka kuma nuna cikakken goyon bayansu ga al’ummar Iran.”

Haka nan kuma ya bayyana takaicinsa akan wasu kasashe da su ka kame bakinsu ba ce komai ba akan yin tir da wuce gona da irin abokan gaba, duk da cewa abinda aka yi din keta dokokin kasa da kasa ne.”

Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma kara da cewa; Shirin Nukiliyar Iran na zaman lafiya ne,kuma zai ci gaba da zama a hakan.” Arakci ya bayyana yadda Iran take memba a cikin hukumar hana yaduwar makaman Nukiliya, kuma za ta ci gaba da zama a cikinta.

Akan aiki tare da hukumar hana yaduwar makaman Nukiliya, ministan harkokin wajen na Iran ya ce za su ci gaba da aiki a tare da ita, amma da wata siga ta daban.”

Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma kara da cewa; A shirye muke mu koma aiki da diplomasiyya, amma ya zama wajibi ga daya bangaren su fahimci cewa diplomasiyya ba abinda za a fake da ita ba ne, a cimma wata manufa ta daban.”

Abbas Arakci ya kuma ce, matukar ba a yarda da batun hakkinmu na tace sanadarin urani’um ba, to babu wata yarjejeniya da za a cimmawa.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted