Arakci: Ba  Dukkanin Mutane Ne Amurka Za Ta Ci Gaba Da Dauka Wawaye Ba

Ministan harkokin wajen Iran Dr. Abbas Arakci  wanda yake Magana akan sabin rahoton cibiyar Nazari ta majalisar dokokin Amurka akan asarar jiragen yakin  da ta

ministan harkokin wajen Iran

Ministan harkokin wajen Iran Dr. Abbas Arakci  wanda yake Magana akan sabin rahoton cibiyar Nazari ta majalisar dokokin Amurka akan asarar jiragen yakin  da ta yi a yaki da Iran, ya bayyana cewa Amurka ba za ta iya ci gaba da daukar mutane wawaye ba.

Arakci ya wallafa sakonsa a Shafin X da a ciki ya bayyana cewa; A cikin watan Mayu cibiyar Nazari da bincike ta majalisar dokokin Amurka ta fitar da rahoto da ta bayyana cewa; Iran ta rusa da lalata jiragen yakin Amurka 42, yanzu kuma sun ce adadin jiragen da Iran din ta rusa sun kai 81.”

Arakci ya ce; Adadin asara ta hakiki da Amurka ta yi, ya fi haka.”

Arakci ya yi tamaba cewa; Kana son dalili akan hakan?

To dalili ne yadda Babbar cibiyar bayar da umarnin soja ta Amumra “CENTCOM” ta hana dan majalisar dattijai ziyartar sansanoninta tare da cewa suna nan lafiya.”

A karshe Arakci ya ce; Amurkan ba za ta ci gaba da bugar da mutane ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted