Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya aike da sakon jaje da kuma yin Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai kan gidan Mas’ud Barazani tsohon shugaban yankin Kurdestan na kasar Iraki a yau.
Araghchi ya bayyana harin da cewa aiki ne na ta’addanci, kuma Amurka da Isra’ila sun saba aiwatar da irin wannan aiki musamman domin haifar da fitina a tsakanin al’ummomin yankin da suke zaune lafiya da juna.
A nasa bangaren Fira ministan kasar Iraki Shia Alsudan ya kirayi Barazani ta wayar tarho, inda ya jajanta masa tare da tabbatar da cewa tuni ya bayar da umarnin kafa kwamitin bincike kan lamarin.
A yau ne aka kai hari da jirgi maras matuki a kan gidan Mas’ud Barazani da ke yankin Dahuk a kasar Iraki, lamarin da ke nuni wani boyayyen shiri na haifar da wata fitina a cikin kasar ta Iraki.