Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Rome na kasar Italiya a ranar Asabar mai zuwa.

M. Araghchi ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin kasar na mako-mako yau Laraba cewa, inda ya ce taron na Rome zai kasance gabanin wani taro a ranar Juma’a na tsakanin Tehran da kasashen Turan nan uku da ake wa lakabi da E3 wato – Ingila, Faransa da kuma Jamus wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015.

Ya ce rawar da kasashen Turai uku ke takawa ta ragu sakamakon manufofinsu a tattaunawar da aka dade ana yi, don haka a shirye muke mu gudanar da zagaye na gaba na shawarwari da su a birnin Rome.

Babban jami’in diflomasiyyar ya kara da cewa, Tehran na da burin warware batun nukiliyarta cikin lumana.”

Da aka tambaye shi game da halin da ake ciki na baya-bayan nan na kudaden da Iran ta toshe saboda takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata, Araghchi ya ce daskararrun kudaden na daga cikin takunkumin da ya zama dole a dagewa iran.

Kawo yanzu Iran da Amurka sun yi tattaunawa har uku ta farko a Oman, ta biyu a Italiya sai kuma wace aka gudanar a ranar Asabar data gabata a Oman.

Dukkanin bangarorin na cewa akwai fata mai kyau a jerin tattaunawar da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments