Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya soki kasashen nan guda uku na turai game da matakinsu na baya baya nan a game da shirin nukiliyar Iran.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da ta yi da takwararsa ta Birtaniya Yvette Cooper, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya jaddada sha’awar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na shiga tattaunawa bisa girmama hakkn kasa, yayin da ya yi watsi da duk wata hanya da ta dogara da matsin lamba na gefe daya.
Ya jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba yin watsi da tattaunawa ba idan aka yi la’akari da girmama hakki da muradun al’ummar Iran, amma ya bayyana karara cewa Tehran ba za ta amince da tattaunawar tilasta wa bangare daya ba.
Wannan na zuwa na a daidai lokacin da ake kara samun tada jijiyoyin wuya bayan wani matakin da kasashen uku na Turai suka dauka kan yarjejeniyar nukiliya ta 2015 da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda ya kai ga dawo da dukkan takunkuman MDD kan Iran.
Tehran ta yi watsi da wannan matakin wanda ta danganta a matsayin wanda ba bisa ka’ida ba kuma ta nuna ficewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliya a shekarar 2018 da kuma goyon bayan da ƙungiyar Turai ta yi wa takunkumin da ba bisa ka’ida ba da aka sake kakaba wa Iran bayan ficewar Amurka.