Araghchi: Gwamnatin Amurka ta haramta wa Irakawa samun wutar lantarki

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na haramtawa  al’ummar Iraki ‘yancinsu na samun wutar lantarki,

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na haramtawa  al’ummar Iraki ‘yancinsu na samun wutar lantarki, da ma wasu ababen more rayuwa.

“Muna tare da al’ummar Iraki, kuma mun tabbatar da alkawarinmu ga gwamnatin Iraki na ba da hadin kai wajen tinkarar matakan da Amurka ta dauka ba bisa ka’ida ba,” in ji Araghchi a wani sakon da ya wallafa a shafin X.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wani babban jami’an makamashi  a kasar Iraki yana cewa, a halin yanzu Iraki ba ta da wasu hanyoyin da za su maye gurbin makamashin da ake shigowa dashi  daga kasar Iran, lamarin da zai haifar da babban kalubale wajen biyan bukatar wutar lantarki a cikin gida musamman a lokacin bazara.

Tun da farko a ranar Lahadin da ta gabata, wani jami’in Amurka ya tabbatar da cewa Washington ta yanke shawarar kin sabunta yarjejeniyar da ta bai wa Iraki damar sayen wutar lantarki daga Iran.

Wani babban jami’in ma’aikatar wutar lantarki ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa “Gwamnati ta fara aiwatar da matakan gaggawa don rage tasirin matakin da Amurka ta dauka kan samar da wutar lantarki a Iraki.”

Wa’adin ya kare a ranar Asabar din da ta gabata, yayin da kumama’aikatar harkokin wajen Amurka ba ta tsawaita wa’adin ba, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin jakadancin Amurka da ke Bagadaza ta bayyana.

Wannan shawarar wani bangare ne na matakin matsin lamba na Shugaba Donald Trump kan Iran, da nufin dakatar da abin da yake kira barazanar nukiliyar Iran, da dakile shirinta na makami mai linzami da kuma hana ta tallafawa kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments