Aragchi Ya Gana Da Grrosi da Kuma Takwaransa Na Kasar Masar

Ministan harokokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Masar da kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya Rafael Grossi a

Ministan harokokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Masar da kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya Rafael Grossi a karon farko tun bayan yakin kwanaki 12 wanda kasashen Amurka da HKI suka kaiwa Iran a cikin watan yunin da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, Aragchi ya kai ziyarar aiki na kwana guda birnin Alkahira a yau Talata ce don tattauna batun shirin Nukliyar kasar Iran da shugaban hukumar IAEA Rafael Grossi a birnin Al-Khahira.

Labarin ya kara da cewa ministan ya ce Iran ta amince ta bude sabon shafi a huldarta da hukumar IAEA bisa wani sabon tsari wanda a cikin iran zata tabbatar da amincin shirinta na makamashin nukliya da kuma kare hakkinta na gasa makamashin uranium kamar yadda ya zo a cikin yarjeniyar NPT babu kare babu ragi.

Har’ila yau ana saran Aragchi zai gana da shugaban kasar Masar Abdulfatta Assi da kuma ministan harkokin wajen kasar a kebe, inda zasu tattauna. Dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments