Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kungiyar tarayyar Turai wacce a halin yanzu ta rasa kimarta ta maida taron tsaro na Munich a matsayin ‘taron makirce’ idan ana maganar Iran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa, ganin yadda kasashen turai suka mika kansu ga HKI, musamman kuma kasashe E3 daga cikinsu, Iran ta gommace ta yi hulda da kasashen yankin, wadanda suke makob taka da ita a kan wadan nan kasashen Turai.
Ministan yace a halin yanzu tarayyar Turai ta zama kungiya wacce bata da wata kima, saboda ba zata iya kaucewa bukatun HKI ba. Don haka a wajen iran kasashen sun ye gefe daga al-amura manya-manya a gabas ta tsakiya.
Ya ce kasar Jamus a halin yanzu tana gudanar da dukkanin al-amuran ta ta yadda HKI take bukata, kuma bata da wani zabi na kanta.
Iran ta sanyawa yarjeniyar NPT ta hana yaduwa makaman Nukliya tun shekara 1970, amma wadannan kasashen turai 3 Jamus Faransa da Burtania sun dake sun sun hanata hakkinta na amfani da makamashin nukliya ta zaman lafiya wanda yarjeniyar ta amince mata.