Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, daga yanzun kuma jajayen layi sun kare, idan Amurka da HKI sun sake farwa kasar Iran da yaki.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka a shafinsa na X, a safiyar yau Asabar ya kuma kara da cewa, sojojin JMI a shirye suke tsab don murkushe duk wanda yake farwa kasar da yaki. Kuma barnan da sojojin Iran zasu yiwa duk wanda ya sake takalarta sai ya dara euro biliyon 100 wanda Merz yake magana kan asarorin turai a yakin.
Labarin ya kara da cewa ministan yana maida martani ne ga Chancellor na kasar Jamus Friedrich Merz wanda ya bayyana a birnrnin soul na kasar Korea ta kudu kan cewa mai yuwa kasashen Amurka da HKI su sake farwa kasar Iran da yaki. Ya kuma kara dacewa yakin ya haddasawa kasashen turai asarori na tattalin arziki masu yawa.
Merz ya ce, ya zuwa yanzu kasashen turai sun yiasarar euro biliyon 100 saboda wannan yakin. Ya kuma kara da cewa ba za’a warware matsalolin da yakin ya jawo a wani yaki ba, don haka suna kokarin ganin an dawo kan hanyar diblomasiyya. Ya kuma yi kira ga bangarorin biyu su dawo kan teburin tattaunawa da diblomasiyya.
==== =====.
Wani Babban Jami’an Tsaro A Iran, Yace: Taddanci Da Yaki Ba Zai Kare A Banza Ba
Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Janar Mohsen Rezaie, ya bayyana cewa, ayyukan ta’addan da kuma takalar yaki ba zai kare a banza ba, don hake ne kasashen Turai da Amurka suke cikin mummunan halin tattalin arziki a lokacinda JMI ta refe mashigar ruwa ta Hurmuz.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rezaei yana fadar haka a matsayin maida martani ga Chancellor na kasar Jamus Friedrich Merz wanda yake fadar cewa kasashen Turai sun yi asarar akalla euro billion 100 saboda yakin yake yaken da Amurka da HKI suka dorawa JMI a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Yakin ta’addanci wanda kasashen biyu suka farwa Iran da shi shi ne na kwanaki 12 daga ranar 13 ga watan Yunin shekara ta 2025 zuwa 24 ga watan. Inda suka kashe saho na farko na jami’an tsaron kasar Iran daga ciki har da ministan tsaro da kwamnadojin sojojin kasar da masana fasahar Nukliya. Sai kuma na biyu wanda suka fara a ranar 28 ga watan Fabrairun shekara ta 2026. Inda a rana da farko suka kashe mutumi na farko a kasar Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminaei (a) da iyalan gidansa a cikin gidansa. A wannan karon ma sun kashe wasu karin manya manyan jami’an tsaron kasar daga ciki har da ministan tsaro da kuma manya manyan kwamandojojin sojojin kasar. Yakin ya dauki kwanaki 40 cur ana fafatawa. Maida martanin sojojin Iran ya tilastwa makiya bukatar a tsagaita wuta. Wanda aka sanyawa hannu a ranar 17 ga watan Yulin shekara ta 2026.
Sannan bayan makonni Am,urka ta karya alkawalin Islamabad ta sake farwa kasar Iran da wani yaki a kudancin kasar, don bude mashigar ruwa ta Hurmuz na tsawon kwanaki 13,a nan sojojin Iran sun lallasasu a wurere da dama a yankin. A lokacin kasashen Turai musamman kasar wazirin kasar Jamus Merz ya ce Amurka da HKI suna masu “mummunan ayyukansu” yana goyon bayan yakin. Don haka Rezaei yace: a yanzun ku dandana dacin abinda hannayenku suka aikata.