Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kasar Iran ba zata taba amincewa da dakatar da tache makamashin uranium a cikin gida ba, saboda yana daga cikin gagarumin ci gaban da kasar ta samu a cikin shekaru kimani 50 da suka gabata, don haka ne batun dakatar da shi kwata-kwata baa bin tattaunawa da makiyan JMI ba, amma muna iya tauuata kan yawansa.
Iran dai ta sami gano fasahar tache makamashin Uranium a kasar A shekara ta 2006 kuma ya zuwa yanzun ta na amfani da fasahar a bangaroriun ci gaban kasar da dama. Daga ciki har da samar da wutan lantarki, magunguna, bunkasa ayyukan noma da sauransi.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana cewa, Iran ba zata amince da bukatar Washington na dakatar da tache makamashin uranium a cikin giuda ba, kuma a shirye take ta kutsa cikin yaki da Amurka don kare hakkinta na yin haka wanda ya zo a cikin yarjeniyar NPT.
Kafin haka dai Iran ta cimma yarjeniyar JCOPA wacce ta bada damar tache makamashin Uranium takaitacce don bukatunta, wanda kuma bai za zai kaita ga mallakar makaman nukliya ba.
Amma turump ya fidda Amurka daga yarjeniyar a shekara ta 2018 sannan ya takurawa kasar ta takunkuman tattalin arziki mafi tsanani a tarihin wata kasa a duniya. Daga karshe ta farwa kasar da yaki a cikin watan Yunin da ya gabata. Sannan da ita da HKI sun kashe masana fasahar Nukliya na kasar da dama don cimma wannan manufar amma sunkasa cimma manufofinsu.