Arachi: Amurka Ta Zabi ‘Dokokin Daji’ Kan Daplomasiyya

Manistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin Amurka ta zabi salon rayuwar dabbobi a daji, kan diblomasiyya inda ta koma ga

Manistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin Amurka ta zabi salon rayuwar dabbobi a daji, kan diblomasiyya inda ta koma ga amfani da karfi da kuma takunkuman tattalin arziki don cimma manufofinta a duniya.   Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a makon da ya gabata a gaban daliban da malamansu a jami’ar MGIMO a kasar Rasha, wanda ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yada labarin a yau Jumma’a.

Aragchi ya kara da cewa, abin bakin ciki duniyarmu ta kama hanyar ko tafrkin rashin doka da oda. Ya kara da cewa: Bayan an kama majalisar dinkin duniya bayan yakin duniya na biyu, kasashen duniya sun yi kokarin kawo tsari bisa kafa dokoki ka’idojin kasa da kasa, amma a bin bakinciki abubuwan da muke ganin suna faruwa a yau, musamman a tsarin da gwamnatin Amurka take bi, yin watsi ne da dokokin kasa da kasa, da kuma maye gurbinsu da karfi soje da karfin tattalin arziki.

Ministan yace tsarin shugaban Amurka Donal Trump a halin yanzu shi ne ‘Zaman lafiya tare da amfani da karfin soje’ a yayinda kasashen duniya sun dade suna kokarin tabbatar da zaman lafiya ta hanyar diblomasiyya da kuma dokoki. Yace: Zaman lafiya tare da amfani da karfi, yana nufin duk wanda yafi karfi zai tursasawa wadanda ya fisu karfi manufofinsa’ wannan kuma shi ne dokokin rayuwar dabbobi a daji.  Ministan ya kammala da cewa, ‘ba kawai washingtong ta na kaiwa kasashe hare-hare a duk lokacinda taga dama ba, tana bawa HKI dashenta a cikin kasashen Asiya damar kai hare-hare kan duk kasar da ta ga dama a yankin. Tana keta dokokin kasa da kasa a duk lokacinda ta ga damar yin haka.   A cikin shekarun da ta gabata HKI ta kai hare hare kan kasashe da dama, sannan ta kashe dubban falasdinawa a Gaza, kuma tana ci gaba da kisan kiyashi tare da tallafin Amurka da wasu kasashen turai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted