Sayyid Abdul-Malik al-Houthi, shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen ya ja kunnen Amurka da HKI kan kara tada hankali a yankin Asia ta kudu.
Kamfanin dillancin labaran IP ya nakalto shugaban yana fadin haka a jiya Alhamis, a lokacinda yake jawabi ga mutanen kasar jawabinsa na mako mako.
Sayyid Huthi ya bayyana cewa kasashen biyu suna son ci gaba da yiwa wadan nan kasashen mulkin mallaka, da kuma mamayarsu. Yace: HKI ba abinda take so in kara fadada kasarta don kaiwa ga gurinta na Isra;ila babba, ya kamala da cewa kasashen biyu suna son tababatar da cewa tunaninsu na mulkin mallaka da kuma ci gaba da sace arzikin yankin.
A wani bangare na Jawabinsa, Sayyid Huthi ya bayyana cewa, sojojin lasar Lebanon basu isa su kare kasar Lebanon daga mamayar HKI ba, don haka manufar kwance damarar kungiyar hizabullah wanda gwamnatin kasar Lebanon suka yi shi ne bawa HKI ta mamaye kamar Lebanon karo na biyu tare da Kenan.
Don haka da yardarm All.. Amurka da HKI da kuma ba zasu sami nasara a kan kungiyar da kuma mutanenn kasar Leabanonba.