Da safiyar Alhamis ne jiragen yakin HKI su ka kai jerin hare-hare akan birnin San’aa da Hudaidah dake yammacin kasar Yemen.
Tashar talbijin din ‘almayadin’ mai watsa shirye-shiryenta daga birnin Beirut na kasar Lebanon, ta ce sojojin HKI ta kai hare-haren ne sau 6 a kasar ta Yemen.
Hare-haren sun shafi tashar jirgin ruwan ta Hudaida, da kuma cibiyar man fetur ta “Ra’asu-Isa” dake yammacin kasar ta Yemen.
Rahotannin da suke fitowa daga Yemen sun ce mutane 6 ne su ka yi shahada sanadiyyar hare-haren na HKI, yayin da wasu da dama su ka jikkata.
Bugu da kari jiragen yakin HKI sun kai wasu hare-haren akan tashar wutar lantarki ta “Zahban” a yankin Arewacin Yemen a birnin Sanaa.
Hare-haren sun yi sanadiyyar tashin gobara, sai dai ma’aikatan kwana-kwana sun yi nasarar kashe ta.
An sami daukewar wutar lantarki a cikin yankuna mabanbanta na babbar birnin kasar Sanaa.
A gefe daya sojojin Yemen sun sanar da kai harin ramuwa da makami mai linzami samfurin “Ballistic” akan birnin Tel Aviv.
Kafafen watsa labarun HKI sun ce harin ya yi barna ta dukiya sannan kuma ya tilastawa ‘yan share wuri zauna da dama gudu zuwa inda za su buya.
Kakakin sojan Yemen Janar Yahya Sari, ya sanar da kai harin na mayar da martani akan Yafa a HKI.
Yemen dai ta ce ba za ta daina kai wa HKI hare-hare ba har sai an daina kai wa Gaza hari, an kuma dauke mata takunkumi.